Matthew 18

Mafi Girma a Mulkin Sama

1A lokacin nan sai almajirai suka zo wurin Yesu suka yi tambaya suka ce, “Wane ne mafi girma a mulkin sama?”

2Sai ya kira ƙaramin yaro ya sa shi ya tsaya a tsakiyarsu. 3Sai ya ce: “Gaskiya nake gaya muku, in ba kun canja kuka zama kamar ƙananan yara, labudda, ba za ku shiga mulkin sama ba. 4Saboda haka, duk wanda ya ƙasƙantar da kansa kamar wannan yaro, shi ne mafi girma a mulkin sama.

5“Duk kuma wanda ya karɓi ƙaramin yaro kamar wannan a cikin sunana ya karɓe ni ne. 6Amma duk wanda ya sa ɗaya daga cikin ƙananan nan da suka gaskata da ni ya yi zunubi, zai fiye masa a rataya babban dutsen niƙa a wuyarsa, a kuma nutsar da shi a zurfin teku.

7“Kaiton duniya saboda abubuwan da suke sa mutane su yi zunubi! Dole irin waɗannan abubuwa su zo, sai dai kaiton mutumin da ya zama sanadin kawo su! 8In hannunka ko ƙafarka yana sa ka zunubi, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka shiga rai da hannu ko ƙafa ɗaya da hannuwa biyu ko ƙafafu biyu da a jefar da kai cikin madawwamiyar wuta da hannuwa biyu ko ƙafafu biyu. 9In kuma idonka yana sa ka zunubi, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka shiga rai da ido ɗaya, da ka shiga jahannama ta wuta da idanunka biyu.

Misali na Ɓatacciyar Tunkiya

10“Ku lura, kada ku rena ɗaya daga cikin waɗannan ƙanana. Gama ina faɗa muku malaʼikunsu a sama kullum suna duban fuskar Ubana da yake cikin sama.
Waɗansu rubuce rubucen hannu na dā suna da sama. 11 Ɗan Mutum ya zo ne domin yǎ ceci abin da ya ɓata.


11
This verse is empty in this translation.
12“Me kuka gani? In wani yana da tumaki ɗari, sai ɗaya daga cikinsu ta ɓace, ba sai yǎ bar tasaʼin da taran a kan tuddai yǎ je neman guda ɗayan da ta ɓace ba? 13In kuwa ya same ta, ina gaya muku gaskiya, zai yi murna saboda ɗayan fiye da tasaʼin da taran da ba su ɓace ba. 14Haka ma Ubanku da yake cikin sama ba ya so ko ɗaya daga cikin ƙananan nan yǎ ɓace.

Ɗanʼuwa da Ya Yi Maka Laifi

15“In ɗanʼuwanka ya yi maka laifi, ka je ka nuna masa laifinsa, tsakaninku biyu kaɗai. In ya saurare ka, ka maido da ɗanʼuwanka ke nan. 16Amma in bai saurare ka ba, ka je tare da mutum ɗaya ko biyu, domin ‘a tabbatar da kowace magana a bakin shaidu biyu ko uku.’
M Sh 19.15
17In kuwa ya ƙi yǎ saurare su, sai ka gaya wa ikkilisiya; in kuma ya ƙi yǎ saurari ikkilisiya ma, ka yi da shi kamar marar sanin Allah ko mai karɓar haraji.

18“Gaskiya nake gaya muku, duk abin da kuka ɗaure a duniya, za a ɗaure a sama, duk kuma abin da kuka kunce a duniya, za a kunce shi a sama.

19“Har wa yau, ina gaya muku cewa in mutum biyu a cikinku a duniya suka yarda su roƙi wani abu, Ubana da yake cikin sama zai yi muku. 20Gama inda mutum biyu ko uku suka taru cikin sunana, a can ma ina tare da su.”

Misali na Bawa Marar Tausayi

21Sai Bitrus ya zo wurin Yesu ya yi masa tambaya ya ce, “Ubangiji, sau nawa zan yafe wa ɗanʼuwana saʼad da ya yi mini zunubi? Har sau bakwai?”

22Yesu amsa ya ce, “Ina gaya maka, ba sau bakwai ba, amma sau sabaʼin da bakwai.
Ko kuwa sabaʼin sau bakwai


23“Saboda haka, mulkin sama yana kama da wani sarki wanda ya so yǎ yi ƙididdigar dukiyarsa da take a hannun bayinsa. 24Da ya fara ƙididdigar, sai aka kawo masa wani wanda yake bin bashin talentii dubu goma. 25Da yake bai iya biya ba, sai maigida ya umarta a sayar da shi da matarsa da yaransa da kuma duk abin da yake da shi, a biya bashin.

26“Bawan ya durƙusa a gabansa. Ya roƙa, ‘Ka yi mini haƙuri, zan biya ka ƙaf.’ 27Maigidan bawan ya ji tausayinsa, ya yafe masa bashin, ya kuma sake shi.

28“Amma da wannan bawa ya fita, sai ya gamu da wani abokin bautarsa wanda yake binsa bashin dinari ɗari. Sai ya cafke shi, ya shaƙe shi a wuya yana cewa, ‘Biya ni abin da nake binka!’

29“Wannan abokin bautarsa ya durƙusa ya roƙe shi, ‘Ka yi mini haƙuri, zan biya ka.’

30“Amma ya ƙi. A maimako, sai ya je ya sa aka jefa shi a kurkuku, sai ya biya bashin. 31Saʼad da sauran bayin suka ga abin da ya faru, abin ya ɓata musu rai ƙwarai, suka tafi suka faɗa wa maigidansu dukan abin da ya faru.

32“Sai maigidan ya kira wannan bawa ciki. Ya ce, ‘Kai mugun bawa, na yafe duk bashin da nake binka domin ka roƙe ni. 33Ashe, bai kamata kai ma ka ji tausayin abokin bautarka yadda na yi maka ba?’ 34Cikin fushi, maigidan ya miƙa shi ga maʼaikatan kurkuku su gwada masa azaba, sai ya biya dukan bashin da ake binsa.

35“Haka Ubana da yake cikin sama zai yi da kowannenku, in ba ku yafe wa ʼyanʼuwanku daga zuciyarku ba.”

Copyright information for HauSRK